Spread the love

Mutum ɗan shekara 42 Ejiro Patrick a ranar Laraba an zarge shi da ya bugi matarsa ta mutu a cikin al’ummar Tyomu a garin Makurdi ta jihar Benue.

Shedun gani da ido ya ce Patrick wanda yake ɗan asalin jihar Delta ne ya tuhumi matarsa ba ta ba shi 5000 ɗin da ta sayar kayansu ga danginta.

Ya ce a cikin fushi ya farmata har sai da ta mutu.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Benue DSP Catherin Anene ya ce mutumin masunci ne yana cikin homar ‘yan sanda a tsare.

Anene ya ce mutumin ɗan Delta ne amma ita matar ‘yar jihar Benue ce an samu hatsaniyar ne a bakin gulbi saboda matar tasa ta sayar da wasu kaya ga danginta ba ta ba shi kudin kayan ba 5000.

Ya bugi matar sai da ba tasan in da take ba a tafi da ita asibitin koyarwa ta Benue can aka tabbatar ta mutu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *