Spread the love

Wani mutumi dan shekara 55 mai suna Chike Eze, ya roki wata kotu dake jihar Legas akan ta raba auren shi da matar shi kafin ya kashe ta.

A bayanin da ya yiwa kotu, Mista Eze ya bayyana cewa babu wata soyayya da ta rage tsakaninsa da matarshi mai suna Rachael, kuma yana so a raba aurensu cikin gaggawa.

Mai koken a lokacin da  ya bayyana a gaban kotu ranar Litinin 10 ga watan Fabrairu, Eze ya roki kotun ta raba aurensu don hakan ita ce hanya daya da za ta kare shi daga aikata kisan kai.

A cewarsa fiye da shekaru biyu kenan bai kara samun kwanciyar hankali a cikin gidanshi ba.

“Ta kai ni ga bango, idan har zan mayar da martani zan kashe ta ne. Ban son na aikata kisan kai, saboda banson a kamani da laifin kisan kai. Abin da ya fi shi ne kotu ta raba auren mu, kowa ya kama gabansa.

“Tana yawan dukana da abubuwa masu hadari, wadanda suka na samu raunika da yawa a jikina. Kullum sai ta rinka  ta zagina.

 Ta taba fasa mini tayoyin mota, ta kuma yaga mini tufafina a lokuta da dama.

“Abu na karshe da ya hada ni da ita, ta dauki mudubi  ta jefe ni da shi, mudubin ya same ni ya yi mini mummunan rauni a kafa. Na samu tabo da yawa a jikina saboda abubuwan da take kai mini hari da su,” Eze ya bayyanawa kotu.

Ya gabatar da hotunan raunukan da ta ji masa a gaban kotun a matsayin shaida. Ya kuma koka kan  matar ta shi tana yawan fita ba tare da neman izininsa ba, kuma duk lokacin da yayi mata magana sai ta ce jikinta ne tana da iko ta yi duk abinda take so.

Sai dai kuma a  bangaren, Rachel ta karyata duka wadannan abubuwa da mijin nata ya fada.

A karshe alkalin kotun ya daga sauraron karar zuwa wani lokaci, domin a dawo a cigaba da sauraren karar ko kila ma a yi masu bahasi tsakaninsu don tsakanin mata da miji sai Allah.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *