Spread the love


Daga Kwairi Waziri Hashidu.

Wasu mahara da ake kyautata zaton ‘yan Boko Haram ne, sun kai hari a unguwar Jiddari Polo, da ke cikin babban birnin Maiduguri. 
Wannan sabon harin, ya zo bayan awa biyu, da shugaban kasa Muhammadu Buharin ya bar birnin Maiduguri, inda mayakan suka kai farmaki unguwar a daidai lokacin sallar magariba.
Kamar yadda wakilin leadership, ya tattauna da jama’a da dama a unguwar, daga ciki akwai Malam Shettima Umar wanda ya bayyana cewa, ”yanzu haka sai karar harbe-harben manyan bindigogi, jama’a kuma suna ta gudu  kowa ta kansa yake yi”.
Gaskiya al’amari ne mai daure kai, ganin cewa harin yazo yan awanni kadan, da ziyarar shugaban kasa Muhammadu Buhari, yayi a nan birnin Maiduguri. 
Wannan wane irin abu ne haka, wane laifi muka yi ne haka da har bamu cancanta mu samu kwanciyar hankali ba.
Wasu bayanan kuma sun tabbatar da cewa, kararar bindigogin tana dan lafawa, sannan kuma jami’an tsaro na ci gaba da kai dauki a unguwar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *