Spread the love

Ihun ba ma so, ba ma yi da muka ji ana yi cikin wani bidiyo da ke nuna tawagar Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ce aka yi wa a lokacin ziyarar jaje a Maiduguri

Koma dai wanene ake wa irin wannan ihun akwai abun dubawa. Kenan al’umma sun fara kosawa da irin yadda harkar tsaro ta lalace? Kenan darajar masu daraja ta fara dusashewa? Kenan tsoron masu ban tsoro ya fara lafawa? 
Tunda kuwa har a kazo wannan yanayi da ake yiwa tawagar shugaban kasa ihu a garin Maiduguri, hakan wata manuniya ce dake zama tamkar hannunka mai sanda ga sauran shugabannin da farin jininsu baikai nasa ba.  
Duk da cewa ana ganin ihun da wasu suka yiwa tawagar shugaban kasan bai dace ba, hakan baya rasa nasaba da yadda wasu ke ganin gazawar gwamnati wajen magance matsalolin tsaro wanda yaki ci, yaki cinyewa musamman a arewacin Nijeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *