Spread the love

Sama da ma’aikata dubu 10 da gwamnatin Sanata Bindow ta dauka aiki, gwamnatin Ahmad Fintiri ta kora kan zargin kin bin doka da ka’idojin daukar aiki a lokacin da aka dauki ma’aikatan sun gudanar da zanga-zangar lumana a garin Yola.

Duk da jami’an ‘yan sanda sun mamaye manyan hanyoyin birnin musamman hanyar da za ta kai mutum zuwa gidan gwamnati da majalisar dokokin jiha don su tare masu zanga-zangar da ke dauke da allunan kokensu.

In ana iya tunawa Gwamna Fintiri yana fara kama aiki a matsayin gwamnan ya ba da sanarwar dakatar da aikin da wanda ya gada ya dauka a Satumbar 2018, kan rashin bin doka da ka’idojin daukar aiki.

Ma’aikatan da abin ya shafa suna kira ga abiya su albashin da suke biya bashi, bayan da kwamishinan yada labarai Dakta Umar pella ya ba da sanarwar korar ma’aikatan ne sai suka kira zanga-zangar lumana a Litini data gabata.

Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan jiha DSP Suleiman Nguroje ya ce sun gargadi masu zanga-zangar domin suna shirin kawo tashin hankali.

Shugaban ma’aikatan jiha Dakta Edgar Amos ya ce wadan da aka korar ba su kai dubu 10 ba, sannan daukar da aka yi masu na tattare da kurakurai ne.

Ya ce gwamnati na shirin daukar ma’aikatan da suka cancanta a bangarori da dama. Za ta dauki malamai 2000 a makaratun furamari, da kuma ma’aikatan lafiya da suka hada da likitoci da ma’aikatan lafiya da unguwar zoma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *