Jam’iyar APC a matakin kasa ta fitar da cewa shhugaban kasa Muhammadu Buhari da shugabannin jam’iyar sun sake bitar mambobin kwamitin sasanci da sanya yin aikin sasanta rikicin da ya dabaibaye jam’iyar.

Rahotanni sun nuna rikici ya dabaibaye jam’iyar a jihohi da dama har da jihar Edo in da shugaban jam’iyar na kasa ya fito.

A bayanin da mai magana da yawun jam’iyar Malam Lanre Issa-Onilu ya fitar aka rabawa manema labarai ya ce an kafa kwamitin mutum 12 karkashin jagorancin tsohon Gwamnan Osun Bisi Akande, wanda zai yi masa sakatare Sanata John Enoh. Akande ya maye madadin Sanata Ahmad Lawal da aka sanya aikin a farko.

Sauran mambobin kwamitin sun hada a Gwamnan Neja Sani Bello da Gwamnan Osun Oyetola da jagoran majalisar dattijai Sanata Yahaya Abdullahi da mataimakin kakakin majalisar wakilai Idris Wase da Sanata Tanko Almakura da Sanata Kashim Shattima da karamin ministan muhali Sharon Ikeazor da Alhaji Nasiru Aliko Koki da Sanata Khairat Gwadabe da Sanata Binta Garba.

Lanre ya ce kwamitin ana son ya magance duk wani bambance da ke tsakanin mambobin jam’iya da kawar da rikicin da ke tsakani don karfafa jam’iyar hadin kai ya dawo cikinta.

Akwai matukar wahala kwamitin ya samu nasarar da ake bukata ganin yanda rikici ya yi nisa a jam’iyar, wasu rikicin ma ba su fito fili ba aka gansu sai bayan da jam’iyar za ta yi zaben shugabanninta na kasa da jihohi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *