Spread the love

Gwamnatin Nijeriya ta shawarci marasa aiki da suka kare jami’a suke da kwalin digiri su dakatar da neman aiki mai tsoka na alfarma, ta roke su da subi hanyar da ta dace su samu aikin da za su yi domin dogaro da kansu.

Bayani ne da aka fitar jiya a karkashin ofishin ministan kwadago da samar da aikin yi Chris Ngige ya ba da wannan shawarar ce a Benin jihar Edo, a taron masu ruwa da tsaki kan yawan jama’a da neman aiki mai tsoka a tsakanin masu digiri a manyan makarantun Nijeriya.

Minista ya samu wakilcin daraktan aiyukka na musamman da cigaban aiyukka a ma’aikatar Martina Nwordu ya yi kira ga ‘yan Nijeriya su ga komai har da aiki mai tsokar.

Ya ce matasan da suka fi kowa kudi a duniya shekarrunsu tsakanin 21 zuwa 31 ne ba su taba aikin gwamnati ba amma gwananni ne a kasuwanci da suka ajiye kansu ga samar da abubuwan basira daban daban.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *