Spread the love

 

“Yafi dacewa mu  cire tsoro mu fadi gaskiya,  tun ranar da aka rantsar da ni a kan kujerar gwamnan jihar Borno, ‘yan Boko Haram sun kai hare-haren ta’addanci sau 6 kenan a garin nan Auno,” 

Ya ce “Wani abu kuma kan janyewar sojoji ban raina kokarin da rundunar sojojin Najeriya ke yi ba, anma dai muna rokon rundunar sojan Najeriya ta samar da wani yanki nata a garin Auno, saboda sojoji suna garin Auno anma da zarar karfe biyar 5 na yamma ta yi za su rufe wajen aikinsu su rufe mutane su tashi su koma cikin garin Maiduguri., wannan kuma ba daidai ba ne” a cewarsa.Gwaman Zulum ya ziyarci Auno a jiya da safe ya ce mutanen da aka kashe sun fi 30, duk da kwamandan sojoji ya sanya kididigar mutanen kan mutum 10.Gwaman a jawabin da ya yi kwamadan lafiya dole Sunday Igbinomwanhia a wurin da ‘yan ta’addan suka kawo hari.

Kwamadan a jawabinsa ya ce sojoji sun sadaukar da kansu a wajen kare rayuwa da kayan mutane a jihar. Ya ce rundunar tana wurin wani aikin ne wani wajen lokacin da ‘yan ta’adar suka kawo harin.Ya ce dagangan sojoji ba za su bari ‘yan ta’adda su zo su kashe mutane ba.Ya yi kira ga mutanen gari su bayar da bayanin gaskiya ga sojoji don su kara kare su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *