Spread the love

Kungiyar Dattawan Arewa sun ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kasa a Nijeriya, sun ce talauci musamman a arewacin Nijeriya, rashin kayan more rayuwa ya karu a karkashin gwamnatinsa.

Kungiya ta tunatar da ‘yan Nijeriya kafin zaben 2019 a gargadin da suka yi na rashin kwarewar Buharin.

Kungiyar ta fahimci dangantakar rashin tsaro da talauci abu ne tsayayyaye, amma gwamnatin Buhari ba ta fitar da wata basira ga abin da zai shawo kan matsalar ba.

Kungiyar ta nemi a samu hada hannu tsakanin jami’an tsaro da mutanen gari shugabanni da duk wanda abin ya abin ya shafa da ke da kwarewa da mutunci da rikon amana ya taimakawa jami’an tsaro ga magance matsalar tsaro da ta addabi kasar nan.

A taron manema labarai da aka gudanar a Zariya shugaban kungiyar Farfesa Ango Abdullahi ya sanar da matsayarsu ta hannun Dakta Hakeem Baba Ahmed.

Ya ce Kungiyar sai da ta gargadi mutanen Nijeriya kan rashi kwarewar Buhari kafin zaben 2019.

A martanin da fadar shugaban kasa ta fitar ta bayyana kungiyar a matsayin kwashi kwaram din kungiya kamar Janar na soja da bai da rundunar yaki.

Mai magana da yawun shugaban kasa Femi Adesina a bayanin da ya fitar ya ce a zaben da ya gabata ‘yan Nijeriya ba su jiran wani Damisar takarda ya fada masu wani abu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *