Spread the love

Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar a jiya ya yi kira ga shugabannin Nijeriya su ƙara yin wani abu don fitar da ƙasar cikin matsalolin da take fama da su a ysnzu.

Ya ce ‘yan ƙasar suna cikin matsanancin lokaci.

Ya yi magana ne a wurin bukin cikar sarkin Zazzau Shehu Idris shekara 45 saman karagar mulki a Zariya jihar Kaduna.

Ya ce sun zo ne don su yi wa sarki addu’a Allah ya saka masa da alheri ga jagorancinsa ba ga mutanen Zazzau ba ga ƙasa baki ɗaya. Da godewa malaman addini ga faɗakarwar da suke yi na a koma ga Allah a duk halin matsi da aka shiga.

Ya yi kira ga shugabanni da su ƙara tausayawa talakawa, kowa ya san ana cikin halin ƙunci, ba abin da ya fi ƙarfin Allah, za mu cigaba da yin addu’a kuma za mu yi wa shugbanninmu addu’a.

Ya roƙi mutane su riƙa yi wa shugabani addu’a a kowane mataki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *