Spread the love

Mutum uku aka kashe yayin da mutum 50 suka samu rauni a harin da ‘yan bindiga suka kai wa al’ummar Grumana a ƙaramar hukumar Shiroro jihar Neja a jiya.

Shugaban ƙaramar hukumar Shiroro Alhaji Suleiman Chukuba ya faɗawa waƙilin daily trust an kai harin ne da misalin ƙarfe 4:30 na marece harin shi ne na biyar da aka kawo cikin wannan shekarar.

Ya ƙara da cewar sama da shanu 300 ne aka sace ga hannun fulani, maharan sun yi wa jama’a zobe suna saman babura kusan 100 suna harbi ta ko’ina saman iska don sanar da zuwansu.

Ya ce bai iya ƙididdige yawansu amma jama’a sun ce sun saman babura kusan 100 kowane babur mutum uku ne samansa.

Ya ce yanzu haka kusan mutum 15 ne aka tafi da shi asibitin Mina don kula da su, sauran a duba su gida an ba su magani. Cikin waɗanda suka samu rauni har da ‘yan sa-kai su biyar.

A satin da ya gabata shugaba Buhari ya ba da umarnin a tarwatsa maɓuyar ɓatagarin dake jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *