Spread the love

‘Yar wasan Hausa Maryam Booth ta ce tana sane da faifan bidiyon da aka fitar kanta wanda dimbin jama’a suka kalla.

Ta ce ta so ta yi shiru da bakinta har jami’an tsaro su gama tattara bayani da binciken da suke yi, amma a bayanin da wani mutum ya fitar mai suna Ibrahim Ahmad Rufa’i wanda aka fi sani da Deezell ya sa dole sai ta yi magana a matsayinta na mace ‘yar wasa da wasu ke koyi da ita ba za ta bari maganar ta wuce haka nan ba.

Ta fitar da bayanin a lokutta da dama yana tsoratar da ita kan zai saki bidiyon in ba ta ba shi kudi ba, tsohon saurayinta ne, ta yi kokarin kare mutuncinta amma abin ya faskara ba da saninta ba aka fitar da wannan bidiyon da aka dauka shekara uku da suka gabata.

Ta ce tana nan tana shawara ta dauki matakin hakkinta ga doka kan wanda ya yi mata haka.

Managarciya ta samu bayanin ne a turakar ‘yan wasan Kannywood da suka wallafa a madadin Booth.

Deezell ya karyata zargin shi ya fitar da bidiyon a turakarsa ta Instagram ya ce bayanin da ake yadawa na shi ya fitar da hoton bidiyon ba gaskiya ba ne, wasu ne kawai ke son bata mashi suna suke danga ta shi da fitar da bidiyon.

Ya ce yana son sandar mutane ba shi ba ne kuma bai san wanda ya fitar da bidiyon ba.

“Ni musulmi ne nasan hakan ya sabawa karantarwar Alkur’ani da Manzon Allah Muhammad(S.A.W) ka yada kuskuren wani ga al’umma musamman a kafar sadarwar zamani da zai sanya tashin hankali” a cewarsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *