Spread the love

Jam’iyar PDP reshen jihar Neja ta roki majalisar dokokin jihar ta tsige gwamnan Neja Alhaji Sani Bello kan matsalar tsaro a jihar.

Shugaban jam’iyar a jiha Barista Tanko Beji a bayanin da ya fitar jiya ya ce suna zargin gwamnan ya kasa kuma ba zai iya aiwatar da mafi karancin albashi na dubu 30 ga ma’aikata ba.

Ya ce Gwamna Sani Bello da ke kokarin nuna shi bai yi alkawali a lokacin yakin neman zabensa ba, duk da haka yakamata ya sani karamin abun da gwamnati za ta yi wa mutane ta samar da tsaro na rayuwa da dukiyoyin ‘yan kasa rashin samar da haka jagoran gwamnati ya ajiye mukaminsa ko a tsige shi. bayan wadan nan dayan biyun ba abin da za su amince da shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *