Majalisar kula da tattalin arzikin Nijeriya wadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa ta fitar da fahimtarta cewa al’ummar Nijeriya sun fi tattalin arzikin kasar bunkasa.

Farfesa Doyin Salami da yake jagorantar mutum 8 a majalisar ya fitar da fahimtar a jiya lokacin da suke bayar rahotonsu ga shugaban kasa a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Salami za su shigo ciki tsundum shi da majalisar, in da suka amsa wasu tambayoyi ga shugaban kasa kan wasu kalubale da ake fuskanta da yanda za a shawo kan matsalolin.

Shugaban kasa ya umarci sakataren gwamnatin tarayya ya shawo kan rashin tafiya tare dake tsakanin wasu ma’aikatu da hukumomi.

Ya tabbatar wa majalisar gwamnati za ta yi aiki da shawararsu kan tattalin arziki da wasu lamurra na daban

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *