Spread the love

Hukumar zabe a Nijeriya ta sanya ranar da za a gudanar da zaben Gwamna a jihohin Edo da Ondo.

Ciyaman na hukumar zabe Farfesa Mahmood Yakubu a lokacin da yake yi wa manema labarai jawabi a Abuja ya ce zaben Gwamna a jihar Edo za a gudanar da shi 19 ga watan Satumba, sai na jihar Ondo za a yi shi 10 ga watan Okotoba duk a wannan shekara.

Wa’adin mulkin Gwamnan Edo zai kare 12 ga watan Nuwamba, in da Gwamnan Ondo zai kare a 24 ga watan Fabarairun shekarar 2021.

A tsarin doka ba za a gudanar da zabe sama da kwana 150 kafin karewar wa’adin gwamna mai ci ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *