Spread the love

Shugaba Buhari ya karbi bakuncin gwamnan kanoAbdullahi Ganduje da sauran masu ruwa da tsaki na jihar, ciki har da sarakunan jihar da sauran dattawan jihar. A ganawar tasu Wanda aka shafe awa daya da yan motsi ana tattaunawa,

Shugaba Buhari yace ba zai sa baki a danbarwar da ke tsakanin Ganduje da Sarkin Kano Sanusi ba. Hakan kuwa a cewar shugaba Buhari bai rasa nasaba da bin dokar kundin tsarin mulki da yake bi sau da kafa.

” Buhari yace matukar magana na gaban majalisa ko kotu, shugaban kasa baida damar tsoma bakin sa har sai sun kammala nasu aikin. Dan haka a yanzu ba zai sa baki ba har sai majalisar kano ta kammala aikin ta.

Daman dai ana ganin shugaba Buhari kadai ne zai iya kawo rashin jituwar dake tsakanin Ganduje da Sarkin, yanzu kuma ga abinda shugaba Buhari ya ke fadi

Buhari mai biyar doka da oda ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *