Spread the love

Tsohon Gwamnan Zamfara Abdul’aziz Yari jami’an tsaron ‘yan sanda sun gayyace shi a Abuja kan kalamansa na fusata jama’a  wurin taron siyasa a karamar hukumar Talatar Mafara cikin jihar Zamfara.

Majiyoyin da aka samu sun bayana  tsohon gwamnan ya share tsawon awa shida a wurin manyan jami’an ‘yan sanda a hidikwatar ranar Talata data gabata.

Majiyar ta tabbatar da an gayyaci tsohon gwamna kan jawabinsa da ya yi a ranar Assabar a mahaifarsa a wurin taron magoya bayansa da aka gudanar, ya shigo Zamfara ranar Jumu’a ya koma ranar Lahadi, bayan ya koma Abuja ne jami’an ‘yan sandan suka  gayyace shi.

Ta  bayyana kafin tsohon gwamna ya bar wurin ‘yan sanda sai da ya rubuta takarar yarjejeniyar zai ba da gudunmuwar zaman lafiya a jihar Zamfara.

Da aka tuntubi mai Magana da yawun rundunar ‘yan sanda ta kasa DCP Frank  Mba ya ce ba su  kama Yari ba.

Yace Abdul’aziz Yari ya zo hidikwatarsu ne kan wani abu da ya shafe shi ya gana da shugaban ‘yan sanda Muhammad Adamu.

A bayanin jami’imai kula da yada labaran Yari, Mayowa Oluwabiyi ya ce hukumar ‘yan sanda sun gayyaci tshohon gwamna a matsayinsa na mai biyar doka da oda ya karba gayyatar.  

Ciyaman na jam’iyar APC a Zamfara Alhaji Sani Gwamna Mayanci ya ce ba wata matsala a gayyatar da ‘yan sanda suka yi wa tsohon gwamnan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *