Spread the love

Jam’iyar PDP mai adawa a Nijeriya ta fara shirin gudanar da zaben shugabannin jihohi da yankuna a Nijeriya gaba daya.

Jam’iyar ta ce ta shirya fara sayar da takardun cikewa ga masu sha’awar yin takarar shugabannin jihohi da yankuna, domin zabar sabbin shugabanni da za su tafiyar da jagorancin jam’iyar a wadan nan matakan.

Wannan bayanin an fitar da shi ne a jiya ta hannun Sakataren tsare-tsaren jam’iyar Kanal Austin Akobundu(mai ritaya) ya ce fara sayar da takardun cikewa ya samu amincewa ne a majalisar zartarwa jam’iya a taronta na 88 da ya gudana kwanan nan a Abuja.

Wa’adin shekara hudu na wasu shugabanni a wasu jihohi ya kare a lokaci daban-daban cikin wannan shekara, kan haka yakamata jam’iya ta bi tsarin doka ta zabi sabbin shugabanni jihohin da yankuna a wuraren. A cewar PDP.  

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *