Spread the love

Daga Salisu Magaji Fandalla’fih

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan a yau Alhamis ya kafa kwamitin mutum 56 domin yi wa kundin tsarin mulkin kasar garambawul.

Kwamitin zai kasance karkashin jagorancin mataimakin shugaban majalisar Sanata Ovie Omo Agege.

Sannan kuma ya kunshi wasu manyan jami’an majalisar guda takwas, Sanata daya daga jihohi 36 sannan da mambobi biyu da ga yankuna shida da ake da su a kasar.

Wasu daga cikin mambobin kwamitin sun hada da shugaban masu rinjaye na majalisar Yahaya Abdullahi, da mataimakinsa Farfesa Robert Ajayi Boroffice.

Akwai kuma shugaban marasa rinjaye Eyinnaya Abaribe da mataimakinsa Sanata Emmanuel Bwacha da sauran Sanatocin .

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *