Mahaifiyar Halima Atete

Allah yJa yi wa mahaifiyar Jaruma Halima Atete Rasuwa da safiyar yau a asibiti a Abuja bayan doguwar jinya.

Za’ayi Jana’iza a central mosque Abuja.

Jarumar an daina ganinta cikin sabbin finafinnai wanda wasu ke ganin hakan na da nasaba da rashin lafiyar mahaifiyarta.

Kwanakin baya jaruma Nafisa Abdullahi ta rasa mahaifiyarta, sai kuma jaruma Hafsat Idris ita ma rasa mahaifinta, a yanzu kuma jaruma Halima Atete ta rasa mahaifiyarta, haka sha’anin rayuwa yake mutuwa ta ratsa masana’antar Kannywood ta ɗauki mahaifan jarummai mata uku.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *