Spread the love

Hukumar zabe ta kasa ta soke rijistar jam’iyyu siyasa 74 cikin 91 a Nijeriya kan rashin cika sharudda da ka’idojin cigaba da wanzuwa a matsayin jam’iyar siyasa.

Shugaban hukumar zaben ta Kasa Farfesa Mahmood Yakubu ne ya sanar da haka a taron manema labarai da ya gabatar a Abuja, ya ce a yanzu jam’iyyun siyasa 18 ne hukumar ta sanda su a matsayin jam’iyyar siyasa da ake iya yin takara cikinsu.

A bayanin da ya gabatar jam’iyyu 16 ne ke cikin tsoffin jam’iyyu dayan sabuwa ce aka yi wa rijista, dayan kuwa maganar soke rijistarta yana gaban kotu sai bayan an kammala shari’a.

Yakubu ya ce jam’iyyu 74 suka soke rijistarsu yayin da sukabar 18 ga su kamar haka: .A, A.A, A.A.C, A.D.C, A.D.P, A.P.C, A.F.G.A, A.P.N, N.N.P.P, N.R.M, P.D.P, P.R.P, S.D.P, Y.P.P, Z.N.P

Jam’iyar V.P ita ce sabuwa sai wadda ke gaban kotu A.P.P

Bayan wadan nan jam’iyyu hukumar ba ta san da wasu ba abin da ke nuni da cewa shugabannin jam’iyyun da aka soke za su iya komawa wata jam’iyya kenan don ta sa ta riga ta mutu domin sun kasa cimma bukatar da tsarin dokar kasa a bangaren tafiyar da jam’iyyu ya tanadar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *