Spread the love

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya karbi tawagar matan Gwamnonin Arewa (NGWF) a gidan gwamnati dake Maiduguri a jihar Borno.

A madadin kungiyar matan gwamnonin Arewa, shugabar kungiyar matar gwamnan jihar Kebbi Dakta Zainab Bagudu a cikin jawabinta ta bayyana  godiyarsu ga Gwamna Zulum kan kokarin da yake yi na maido da zaman lafiya da cigaba  in da yake aiki a lungu da sakon a jihar. 

Ta  sanar da gwamnan mambobin taron sun je wasu sansanonin ‘yan gudun hijira waton IDP tare da rarraba kayan ga mata da kananan yara, bayan  lakcoci da aka gabatar kan cututtuka irin  cutar daji ko kansa, da matsalar shan miyagun  kwayoyi a tsakanin al’umma.

Gwamna  Zulum a cikin jawabinsa ya bayyana cewa, kungiyar matan Gwamnonin sun tallafa wajen inganta ilimin yara mata, cigaban mata, kiwon lafiyar mata.

Ya yi kira gare su da su yi amfani da karfinsu a zaman tattaunawa domin samar da wadatattun hanyoyin magance yawon yara kan titi, matakin da ya dace ba tare da nuna bambancin jinsi tsakanin ba.

Yawon yara kan titi da sunan almajirci abu ne da yake damun arewacin Nijeriya, za ka ga yaro dan shekara uku ko hudu ko biyar saman hanya yana gararramba bai san in da za shi ba, uwayensa sun sake shi ga duniya, in ba a dauki mataki ba hakan zai iya zama cikas ga samun bunkasar Arewa a bangaren tarbiya da zaman lafiya.

Managarciya ta goyi bayan kiran da gwamna ya yi abu ne da yakamata a shawo matsalar kafin ta wuce in da ake yanzu, mutane yakamata su fahimci lamarin almajirci da kuma hakkin ‘ya’ya ga uwayensu, abubuwa ne guda biyu masu cin gashin kansu daban-daban.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *