Spread the love

Maigirma shugaban Kasar Nijeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da sabbin jiragen yaki da zasu fara kaddamar da hari ta sama akan ‘yan ta’addan Boko Haram da Masu garkuwa da mutane. 
A gurin kaddamar da jiragen; shugaba Buhari ya roki ‘yan Nigeria da su taya shi da addu’ah, sannan su ba da hadin kai don ganin an shafe ruhin ta’addancin Boko Haram daga doron duniya da duk wani aikin tayar da ƙayar bai a Nijeriya. 
Wannan mataki da shugaba Buhari ya dauka na canza salon dabarun yaki abu ne mai kyau, wato idan yakin kasa ya gagara sai a koma a karfafi yakin sama, abin da Amurka tayi kenan take cin nasara akan abokan gabanta. 

Jiragen an yi bukin ƙaddamar da su a filin taro na eagle square dake Abuja.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *