Spread the love

Uban kasar Gayari cikin karamar hukumar Gummi a jihar Zamfara da aka yi garkuwa da shi a ranar jumu’a data gabata shi da dansa a cikin gidansa in da ake zargin mahara ne suka sace shi, tau an sako shi kamar yadda jaridar daily trust ta samu labari.

Majiyar ya sheda mata ‘yan bindigar sun saki uban kasar ne bayan kwashe kwanaki ana yarejeniya da su kan kudin fansar, tun tashin farko sun bukaci a ba su miliyan 40 daga baya aka dawo miliyan 16, har dai aka cimma matsaya a biya miliyan 5 kafin a sake shi.

Amma dai har yanzu ba ta kare ba don sun rike dansa sai an kawo masu babur guda biyu kafin su sake yaron.

Maimagana da yawun ‘yan sandan jihar Zamfara SP Muhammad Shehu ya tabbatar da sakin uban kasar amma dai ya yi shiru da bakinsa kan an biya fansa ko ba a biya ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *