Hakika a yanzu lokaci ya zo wanda dukkan Al’ummar jihar Zamfara suka dawo daga rakiyar zarge-zargen karya wanda ake yi akan tsohon gwamna jihar Zamfara Abdul’aziz Yari, da ake cewa shi tamkar barazana ne ga zaman lafiya a jihar Zamfara.

Hakazalika tuni gaskiya ta kara bayyana cewar tsohon Gwamna Abdul’aziz Yari ya zamo barazana a siyasar Gwamna Bello Matawalle da kuma jam’iyarsa ta PDP a Zamfara wanda hakan kullum yake kara tsorata gwamnatin jihar ta Zamfara karkashin Bello Matawalle har ma da ita kanta jam’iyar ta PDP.

Tuni Gwamna Abdul’aziz Yari ya riga ya zamo tamkar wata annoba ga dukkan wani shirin makirci na jam’iyar PDP a jihar Zamfara kuma ya zamo abun mafarki da tsoro ga duk wani wanda yake marar kishin jihar ne ko wanda yake cikin tafiyar PDP Zamfara.

Tun daga shi Jagoran PDP na jihar Gwamna Bello Matawalle zuwa wasu ‘yan ƙalilan magoya bayan PDP a jihar sun shiga ɗimuwa da damuwa na ganin yanda tsohon Gwamna Abdul’aziz Yari yake iya kokarinsa kullum ba dare ba rana don ganin an kwatowa Zamfarawa hakkinsu na wanda suka zaba a zabukan baya cikin shirin sake duba hukuncin kotun koli da ake batun gabatarwa akan hukuncin shari’ar zaben Jihar zamfara.

Sannan kuma Abdul’aziz Yari ya zama tamkar wani Dodo da yake baiwa Gwamna Matawalle tsoro a duk lokacin da ya ziyarci jihar Zamfara ganin yanda al’umma suke cincirindo a tituna don kara jaddada goyon bayansu ga Tsohon Gwamna Yari da kuma jam’iyar APC.

Duk wadannan shaci faɗin da ‘yan jam’iyar PDP suke yadawa akan tsohon Gwamna Yari be rasa nasaba da kasawar gwamnatinsu ta PDP wajen magance lamarin da suka danganci matsalolin tsaro a Zamfara.

Yana dakyau al’ummar jihar dama Najeriya baki ɗaya su kara tabbatar da cewar tsohon Gwamna Yari ya zama barazana akan siyasar Bello Matawalle da jam’iyar PDP bawai a lamarin tsaro na jihar ta Zamfara ba.

Ra’ayin: Matasa Masu Kishin Jihar Zamfara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *