Spread the love

Kwanaki kadan bayan da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin tarwatsa mabuyar maharan a jihar Neja, ‘yan bindigar sun kashe mutum daya, in da mutum uku suka samu mummunan raunuka.

Haka kuma kusan mutum 20 ne suka yi garkuwa da su a cikin al’ummar da suka kai wa samamen a Karamar hukumar Bargu dake jihar Neja.

Babban Limamen Sarkin Bargu dake bayar da sallah a masallacin fadar mai suna Malam Habibu yana cikin wadanda aka yi garkuwa da su.

Harin da aka kai ranar Assabar da karfe 5:30 na marece in da maharan suka yi wa al’ummar zobe, sun zo da yawa saman babura dauke da muggan makamai da suka hada da bindiga da adda da yuka suka rika harbi ta ko’ina suka kashe mutum daya suka tafi da wasu 20, wasu uku suka samu rauni a wurin tirmitsin tserar da rayuwa.

Wata majiyar ta ce ba su san Liman yana cikin wadan da aka sacen ba sai ranar Lahadi da masu garkuwan suka kira Sarki suna neman miliyan 20 fansa kafin su saki liman.

An sake ganin maharan sun kai farmaki a Wawa, su 14 ne aka ga sun wuce a garin New Bussa, amma ba su tafi da kowa ba.

Sarki Alhaji Muhammad Haliru a jiya ya kira taron masu ruwa da tsaki don sanin hanyoyin da za a bi a saki wadan da aka yi garkuwa da su da matakin magance matsalar tsaron.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *