Spread the love

Rikici ya ƙara mamaye jam’iyar APC a jihar Edo in da gwamna Godwin Obaseki ya nemi a kama shugabansu na ƙasa Adams Oshiomhole da gaggawa.

Obaseki ya roƙi shugaban ‘yan sanda Muhammad Adamu da shugaban tsaron farin kaya DSS Yusuf Bichi da su kama Oshiomhole kan ƙin biyayya ga umarnin ‘yan sanda na hana rally da kawo hatsaniya a jiha.

A zantawarsa da manema labarai ta hannun mataimakinsa Philip Shaibu a Abuja, ya ce takardar kokensu ce za su ba hukumomin da abin ya shafa, da kira da cewa Oshiomhole ba ya gudanar da zagayen siyasa ba tare da sanar da gwamna mai ci a jam’iyar APC ba.

Yace ya zo Abuja ne domin magana da Shugaban ‘yan sanda DSS don faɗa masu Adams ya karya doka a kama shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *