Spread the love


Shugaban Karamar Hukumar Mulki ta Aliero Alhaji Abubaka Sale Aliero Ya baiyyana cewa karamar hukumar mulki ta Aliero tana ta farko a cikin kananan hukumomi Masu kwanciyar hankali a duk fadin Jihar Kebbi kuma ba komi ya kawo haka ba sai daukar shawarwari tare da gudanar da taro akan tsaro da ake yi a duk  farkon wata  wanda shi ke warware duk wani tarnaki dake kokarin tasowa a fadin karamar hukumar.  Ya kara da cewa a lokacin da yabar mulki kamin ya dawo a sake zabarsa motar zirga-zirga ta ‘yan sanda ta lalace amma yanzu haka anan nan ana kokarin gyaranta domin Jami’an tsaro su samu abin da za su cigaba da amfani da shi domin saukaka ayukkansu a ciki da wajen garin Aliero.
Ya yi wannan jawabin ne a lokacin da Kwamishinan  ‘yan Sanda Jihar Kebbi   Mista Oluyemi Agunbiade ya kawo ziyar aiki a karamar hukumar mulki ta Aliero 

A lokacin ziyarar Oluyemi agunbiade yakai gaisuwa a fadar Maimartaba Sarkin Aliero Alhaji Salihu Mohammadu na biyu ya jinjinawa  mutanen Aliero bi sa ga hadin kai da taimako da suke baiwa Jami’an tsaro a duk lokacin da wani abu ya faru wannan ya nuna yadda garin yake da hadin kai.  Yayi godiya ga Maimartaba Sarkin Aliero bisa ga yadda yake daukar matakin gaugawa ga duk wata shawarar da Jami’an tsaro suka kawo masa 
A jawabin godiya Maimartaba Sarkin Aliero Alhaji Salihu Mohammadu na ll ya  nuna farin ciki da jindadi da wannan ziyarar  dafatar Allah ya maida shi gida lafiya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *