Spread the love

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada tsohon dan kwallon kafa kuma mataimakin mai horas da kungiyar kwallon kafa a Nijeriya Daniel Amokachi a matsayin Ambasadan Kwallon kafa.

Amokachi ya yi wa kungiyar kwallon kafa ta Nijeriya wasa a 1994 da 1996.

Mukamin Ambasada da Buhari ya nada shi zai taimakawa ma’aikatar wasanni da cigaban matasa domin kara zaburar da bangaren wannan yana cikin hobbasar da gwamnatin Buhari ke yi wajen bunkasa wasan kwallon kafa a bangaren matasa mata da maza.

Wannan bayanin ya fito ne a wurin babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa a bangaren yada labarai Garba Shehu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *