Spread the love

Gwamnan Sokoto ya kashe biliyan 19 a haujin  ilmi a wajen ginawa da gyara ajujuwan karatu 948 a makarantu jihar tun sanda ya fara mulki a shekarar 2015 zuwa yau da Managarciya ta kalato labarin, ya gina sabbin ajujuwan karatu 388, an gyara 460 a cikin wannan lokacin.

Gwamnan Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana haka a ranar Lahadin da ta gabata wajen kaddamar da kason gwamnati tare da bayar da kwangiloli ga mutum 200.

 Gwamnan  ya bayyana an  kashe wasu kudin tallafin gwamnatin tarayya na hukumar ilmin firamare da yawansu ya kai biliyan 7.2 da wasu kudin tallafi da aka samar ta ma’aikatar kananan hukumomi da yawansu ya kai biliyan 6 da biliyan 2 a shirin daurewar muradun karni(SDG) in da aka gina ajujuwan karatu ba tare da jiran tallafin gwamnatin tarayya ba.

Shugaban jam’iyar APC a Sokoto Alhaji Isah Sadik Achida a takaradar da ya sanayawa hannu aka rabawa manema labarai ya ce APC ta ji abin da gwamnatin PDP ta fada wai ta kashe biliyan 19 a gina wa da gyaran ajujuwa cikin shekara biyar ta yaya za mu tabbatar da gaskiya, jiharmu na bukatar hakan.

“Kaso da yawa na dalibai suna zaune kan dabe ne suna karbar darasi don ba kujerin zama a cikin ajujuwa, malamai a Sakkwato an barsu baya a wurin karbar albashi, a duk wata sai sun shiga cikin sati na biyu kafin su amshi albashinsu” in ji Sadik Achida.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *