A yau Talata Jami’an tsaro daga jihar Kano sun kama matashin mawakin siyasa dake jihar Katsina mai suna Muhammadu Buhari, wanda aka fi sani da laƙabin “Kosan Waka”.

Kosan waka dai fitaccen mawaki ne, ɗan gani kashe nin Kwankwasiyya, kuma daya daga cikin mawakan Gwamnan Jihar Katsina, wanda yake wakar sa da salon Dauda Kahutu Rarara, da yawan lokaci in ka ji waƙarsa za ka zaci Rarara ne.

Ana zargin kamun da aka yi wa mawakin ba ya rasa nasaba da wata sabuwar wakar sa da ya fitar a shekaran jiya mai taken ‘A WANKI GARA’.

Waƙar ta yi saurin karɓuwa ga magoya bayan Kwankwansiya a Nijeriya an ɗauki salon waƙar shaguɓe ne ake yi wa Gwamna Ganduje, duk da ba in da ya bayyana sunansa sai dai misalin gudanar da rayuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *