Spread the love

Gobara Ta Cinye Gidan Ɗan Majalisar Tarayya Daga Zamfara, ba a samu labarin musabbabin tashin gobarar ba.

Gobarar ta cinye dukkanin gidan dan majalisar tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Gusau da tsafe a jihar Zamfara Honarabul Kabiru Amadu wanda aka fi sani da Mai Palace.

A sanyin safiyar yau Litinin ne wannan iftila’in ya faru a gidansa dake Gusau cikin iyawar Allah ba a samu asarar rayuka ba, amma an samu hasarar dukiya sosai da har yanzu ba a bayyana yawanta ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *