Spread the love

Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta karbo bashin biliyan 220 ga bankin duniya domin ta magance matsalar rashin zuwan yara makaranta da karfafa ilmin farko a jihohi 17.

Karamin ministan ilmi Chukwuemeka Nwajiuba shi ne ya sanar da haka a karshen sati in da ya jero jihohi 13 a cikin Arewa ta Yamma da ta Gabas, sai ya kara jihar Neja da Oyo da Rivers da Ebonyi su ne za su ci gajiyar shirin.

Ya ce kudin za a yi amfani da su cikin shirin nan samar da ingantaccen ilmi ga kowa(BESDA) a wadan nan jihohin da aka ayyana.

Ya ce za a raba kudin ne gwargwadon yanda jiha take fama da yaran da ba su zuwa makaranta, an riga an kammala duk wani shiri gwamnatin tarayya za ta saki kudin.

Ya ce amma jihohi suna da sharuddan da ake son su kammala kafin su samu damar amfana da kudin.

Ya ce a wurin jihohi lamuni ne in da gwamnatin tarayya yake bashi, jihohi za su biya kudin a wurin gwamnatin tarayya babu ruwa a kudin, gwamnatin tarayya za ta mayarda kudin ga bankin duniya.

Gwamnatin tarayya ta fara gudanar da shirin a 2018, haka aka rika aiwatar da shi a jihohi.

Aiwatar da shirin na BESDA 2018 yana cikin matakan cimma sharudda da shirin ya tanadar domin samun cin gajiyar shirin.

Ministan ya gode wa jihar Adamawa da ta soma fara aiwatar da shirin cikin nasara.

A yanzu kididiga ta nuna sama da yara dubu 50 ne ke yawo banza saman hanya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *