Spread the love

An kaddamar da fara zirga-zirgar jirgin sama daga Abuja zuwa Kaduna sakamakon rashin tsaron da ake yawan fuskanta akan titin motar Abuja zuwa Kaduna, kamar yadda majiyarmu ta Premium Times ta rawaito.

Yanzu dai duk wani mai kudi zai iya hawowa jirgin sama daga Abuja zuwa Kaduna ba sai ya jira jirgin kasa ko ya biyo kan titin motar da za a iya kame shi a garkuwa da shi ba.

Su kuma talakawa marasa kudin jirgin sama, sai su cigaba da addu’ar Allah ya kawo musu karshen lamarin sace su da ake yi akan titin.

Su kuma masu garkuwar da za su yi adalci sai su hakura su daina tare mutane a hanyar, tunda yanzu duk wanda ya bi hanyar a mota to talaka ne bai tara komai ba.

Wannan mataki gaskiya ba zai yiwa talaka daɗi ba ganin yanda fargabar tsaro ta’azara a yankin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *