Spread the love

Babbar mota Tirela ta yi dakon baburan masu yin acaba a Lagos kan hana yin acabar da gwamnatin jihar ta yi a wata sabuwar dokar hana yin acaba na babur da keke mai taya uku a wasu manyan hanyoyin jihar.

Haramcin ya fara ne daga jiya Assabar a kananan hukumomi 15 da wasu manyan hanyoyi da gadojin sama kamar yadda gwamnatin jihar ta bayar da sanarwa a satin da ya gabata.

A jiyan da dokar ta fara aiki ba a ga babur saman hanyoyin da aka sanya wa dokar, hakan ya sanya manyan motoci Tirala suka dauko babura tare da masu baburan domin dawowa Arewa asalin mahaifarsu, akwai mutanen Kano da Katsina da Sokoto da Filato da sauransu.

A kalla a jiyan an ga Tirela 7 dauke da baburan a saman hanyar Legas zuwa Ibadan za su bar Legas don dawowa Arewa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *