Spread the love

Daga Mukhtar Halliru Tambuwal Sokoto

Shugaban Hukumar Zakkah da Wakafi Malam Muhammad Lawal Maidoki Sadaukin Sakkwato ya ce akwai bukatar kafafen yada labarai a Nijeriya musamman a Arewa su kara tashi tsaye wajen fahimtar da al’umma hatsarin bara da zama ci-ma kwance wanda sam bai dace ba a cikin al’ummar musulmai ba, halin yana kara sanya jama’a cikin talaucin da suka sanya wa kansu.

‘Gwamnati a jihar Sokoto ta hannun hukumar zakka da wakafi na iya kokarinta wajen taimakawa al’ummar jihar amma saboda halin da suka sanyawa kansu na bara da son cin banza sun kasa bari a tafi gaba, in aka baiwa mutum tallafin da zai je ya kama sana’a domin dogaro da kai sai ya tafi ya cinye abinsa ya kuma sake dawowa neman taimako, addini da al’ada ba su yarda da wannan ba.’

Malam Lawal ya bayyana hakan ne a wajen cin abincin safe da ya kira  kafafen yada labarai a jihar Sokoto a yau Lahadi ya ce  sun Kira wannan cin abincin safe ne  domin su yi godiya kan gudunmuwar da kafafen yada labaran ke bayarwa ga hukumar Zakkah da Wakafi kuma  su ji shawarwari da korafe-korafe in akwai  domin  habaka ayukkan Hukumar.

Mahalarta sun bayar da gudunmuwa ta shawarwari bayan cin abibncin, in da hukumar ta ba su kyautar kayan marmari domin kaiwa iyali a gida. da sanar da su yiwuwar sake kiran wannan zaman in bukatar hakan ta taso.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *