Spread the love

Daga Mukhtar Halliru Tambuwal Sokoto.

Hukumar zakka da wakafi ta jihar Sokoto karkashin jagoranchin malam Muhammad lawal maidoki, Sadaukin Sakkwato ta raba kudaden tallafin magani na wata wata ga dakunan sayar da magani da Asibitocin da take hulda da su don baiwa mabuƙata a jihar.

Shugaban hukumar ya bayyana cewa kudaden da hukumar ke bayarwa don maras lafiyar da suka tabbata ba su iya sayen magani sai a ba su saboda Allah.

Ya bayyana cewa kuɗi ne da gwamnan jihar sokoto Aminu Waziri Tambuwal ke tallafama hukumar dan aiwatar da aikin jinkan al-ummah a duk watan Allah.

Malam Lawal Maidoki, ya yi kira ga wakilan kwamitocin zakka na Asibitocin su ji tsoron Allah akan amanar.

Ya kuma bayyana cewa wasu Asibitoci ukku za su amfana da tallafin magani da Alhaji Murtala Abdulkadir Ɗan’iyan Jarman sokoto ya ba da, yayi kira ga al’ummar Musulmi musamman masu kudi da su ba da tallafin kuma su yi koyi da wannan talikin da yake baiwa hukumar abinci da magani dan tallafawa bayin Allah.

A wannan watan an raba Naira Miliyan biyar ne da dubu Dari bakwai, ga Asibitoci da dakunan sayar da magani 13 a sokoto.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *