Spread the love

MAHAIFIYA:

Yaron ya tambayi mahaifiyar shi :Miyasa ki ke kuka?
Ta ce: Saboda ni mace ce. Sai yaron yace : Ban fahimta ba.
Sai ta rungume shi ta ce : Ba za ka fahimta ba har abada.

Sai yaron ya tambayi mahaifin shi : Miyasa mama take kuka ba tare da dalili ba??
Sai yace : dukkan mata haka suke kuka babu dalili.
Har yaron ya girma ya zama babban mutum baisan dalilin kukan mace ba.

Sai yaron ya tambayi wani mai hikima : Miye dalilin kukan mata ba dalili ?

Sai Yace masa:Yayin da Allah ya halicci mace, sai ya bata kafaɗu masu ƙarfi domin ta ɗauki nauyin duk duniyar nan, ya bata hannuwa masu taushi domin jaririnta ya ji dadin renonta, ya ba ta karfin halin da za ta iya jure wahalar haihuwa, sannan da juriyar bijirewar ‘ya’yan bayan sun girma.
Da karfin halin kula da iyalinta da damuwa da su, ya bata soyayyar yaranta mara yankewa koda suna cutar da ita.

Kan haka ya ba ta HAWAYE da za ta zubar domin rage wahalar wannan nauyin. domin cigaban tafiyar rayuwarta.

Wannan shi ne raunin mace kwara daya : Saboda haka ku girmama hawayen matan duniya koda sunyi shi babu dalili.

An yanke cibiyarka san da ka fito wannan duniya, ….amma alamarta nanan tare da kai domin ka riƙa tuna wannan macen mai girma wadda ta ciyar da kai daga jikinta.

Ya Allah ina roqonka ka sakawa iyayenmu da Aljanna.

Duk abin da ka yi wa Mahaifiya ba za ka iya biyanta ba, kar ka bari ta zubar da hawaye kan baƙincikinka, amma ka yi ƙoƙari ta zubar da hawaye kan farincikinka, domin ka zama mai godiya da ni’imar da ya yi maka na zama ɗa mai uwa da ta fi son ka fiye da kowa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *