Spread the love

‘Yan sandan jihar Kaduna sun kama Fasto James Clement da ya yi garkuwar kansa da kansa bisa karya, in da ya nemi danginsa su biya fansar miliyan biyar a matsayin fansar wai an sace shi an yi garkuwa da shi.

An kama James ne tare da dan kazaginsa wanda yake tsakaninsa da danginsa.

Mai magana da yawun ‘yan sandan DSP Yakubu Sabo a bayanin da ya fitar ya ce Faston dan shekara 37 da dan kazaginsa an kama su ne kan hada bakin yin garkuwar karya.

‘Yan sanda sun ce sun nemi fansar miliyan 5 a wurin dangin James a sakon waya da Otokpa ya tura musu a matsayin wanda za a shirya da su kafin sakin fasto.

Sabo ya ce sun yi kama mutanen ne abisa bayanin da suka samu wurin wasu mutum biyu dake cikin dangin Faston cewar Garkuwar ba gaskiya ba ce.

Sabo ya ce sun gano in da James ya boye kansa a lokacin da ake yarjejeniyar kudin fasarsa da daginsa ta hanyar na’urorinsu.

Kwamishinan ‘yan sanda ya ce za su gabatar da mai laifin gaban kotu da shaidu domin yi masa hukunci yanda batagari za su dauki izna kansa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *