Spread the love

Zauren majalisar waƙillan Nijeriya sun ba da umarni ga shugabannin tsaron ƙasa su yi murabus kan zargin da ake yi sun kasa, matsalar tsaro na ƙara ta’azzara a Nijeriya.

Majalisar dattijai sun yi kira ga Shugaba Buhari ya aiyana dokar ta ɓaci ga sha’anin tsaron ƙasa.

Majalisar waƙillai dake da mambobi 360 jam’iyar APC ke jagorancin majalisar sun nemi shugaba Buhari ya tsige su in sun ƙi yin murabus.

Wannan yana cikin matsayar da aka cimma a lokacin zaman majalisar wanda shugabanta Femi Gbajabiamila ya jagoranta, dukkan sun aminta da ƙudirin mai tsawatarwa na majalisa Muhammad Munguno da ya gabatar na aduba hare-haren ‘yan boko haram a Arewa ta gabas.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *