Daga Datti Assalafiy

Alherin Allah Ya kaiwa Madugun darikar Kwankwasiyya na duniya Maigirma tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Dakta Rabiu Musa Kwankwaso, a yau din nan ya sake tura dalibai ‘ya’yan talakawa karatu zuwa kasashen waje kamar yadda ya saba.

Watannin baya ma ya tura daruruwan dalibai zuwa Kasar Indiya domin su koyi fannoni dabam-dabam na ilmin zamani da likitanci, a yanzu kuma ya tura sabbin dalibai zuwa Kasashen Dubai da Sudan.

A wannan bangare na daukar nauyin karatun ‘ya’yan talakawa Kwankwaso bashi da sa’anni cikin ‘yan siyasar Nigeria, yayi musu nisa sosai, kuma wannan shine sirrin da yasa Kwankwaso ya sace zuciyar miliyoyin al’ummah musamman talakawa.

Hakika Kwankwaso namu ne saboda mai kishin ‘ya’yan talakawa ne, muna tare dashi akan irin wannan babban jihadi da yake yi.

Ina rokon Allah Ya daukaka darajar Baba Kwankwaso, Ya saka masa da Aljannah Madaukakiya Amin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *