Spread the love

Daga Comr Abba Sani Pantami

Kwanan nan Musulmai za su samu garabasar zuwa aikin Hajji a kasar Saudiyya yayin da Zhikrullahi Hassan, sabon Shugaban hukumar aikin hajji a Nijeriya ya yi alkawarin yanke farashin kudin da ake biya.

Hassan ya fadi hakan ne a lokacin da majalisar dattawa ke tantance shi, inda ya bayyana cewa yunkurin zai ba al’umman Najeriya damar zuwa sauke farali.

Zababben Shugaban ya kuma bayyana cewa zai kafa wani shiri na tanadin Hajji ga maniyyata idan aka tabbatar da nadinsa, majalisar dattijai ta amince ya jahoranci hukumar daga yau.

Kamar yadda kuka sani zuwa aikin Hajji na daya daga ciki manyan shika-shikan addinin Musulunci. Hakan ne ya sa duk Musulmi a fadin duniya ke daukar aikin hajjin da muhimmanci sosai.

Abun bakin ciki, sai gashi tattalin arziki, musamman a kasashen da ke tasowa irin Najeriya, ya sanya Musulmai da dama rashin samun damar zuwa kasa mai tsarki don sauke farali sakamakon yawan kudin a ake karawa duk shekara.

Don haka, ga dukkan alamu lokacin da ‘yan Najeriya da yawa za su samu zuwa aikin hajji ya kusa yayinda Zhikrullahi Hassan, zababben Shugaban hukumar aikin hajji na kasa, ya yi alkawarin yanke kudin Hajjin idan majalisar dattawa ta tabbatar da nadin nasa.

Da yake jawabi ga majalisar dattawa a lokacin tantancewarsa, Hassan ya ce kudin hajji yanzu ba abu ne da mutane ke iya biya ba kuma akwai bukatar sake duba lamarin, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Ya yi bayanin cewa irin wannan yunkurin ba zai bari al’umman Najeriya da ke burin sauke farali samun damar yin hakan ba.

Hassan ya kuma ce zai kafa shirin tara kudin hajji wanda zai ba maniyyata damar tara kudi a hankali kafin lokacin hajjin.

Ya kuma bayyana cewa zai tabbatar da ganin an rage yawan kwanakin da yan Najeriya ke shafewa a kasar Sauddiyya a lokacin aikin hajji, inda ya ce yan Najeriya na dadewa da yawa.

Ƙudurorin sabon shugaban abu ne da mutanen Nijeriya mudamman mudulmi ke jira da buƙata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *