Spread the love

Rabi Musa ‘yar shekara 28 ta rasu biayan ta cinnawa kanta wuta a jihar Kano, ba a san dalilin kone kanta da ta yi ba.

Lamarin ya faru a unguwar Sabuwar Unguwa a mazabar Gayawa karamar hukumar Ungoggo dake jihar Kano.

Margayiya Rabi makwabtanta suna ganin sanyawa kanta wuta da ta yi bai da alaka da rigimar dake tsakaninta da kishiyarta wadda mijinta ya aura wata shida da suka wuce a matsayin matarsa ta biyu.

Wata majiyar ta ce margayiyar ta kone kanta tana dauke da juna biyu, ta bar yara 6 a duniya.

Majiyar ta kara da ceawar mijin margayiyar Malam Badamasi Sufyan a lokacin da lamarin ya faru ya tafi masallaci dake kusa da su don yin sallar safe.

Makwabcinsu da ba a bayyana sunansa ba ya ce bayan mai gidan ya dawo gida ya ga halin da matarsa ke ciki ya fito yana kuka yana neman agaji, an shiga a taimaka masa amma aka kasa domin matar ta kone fiye da misali.

Ya ce da yawan mutane makwabta sun san da matsanancin kishi irin na Rabi ta yi ta rigima da kishiyarta tsawon wata shidda da ta shigo gidan. Hakan ya sanya mijinsu ya raba su wuri daya kowace ya kebe ta bangarenta daban.

Ya ce bai iya cewa wannan na da nasaba da kishinta ba.

Jami’in hulda da ‘yan sanda DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da sun samu labarin kuma suna kan binciken abin da ya yi sanadin mutuwar matar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *