Spread the love

Daga Sadiya Attahiru Jabo.

Mutum bakwai har da Hakimin kauyen Tudun Doki a cikin karamar hukumar Gwadabawa Alhaji Hayatu Ardo sun rasa ransu a hadarin mota da ya faru saman hanyar Gwadabawa zuwa Illela a jihar Sokoto.

Mai magana da yawun hukumar kiyaye hadurra ta jihar Garba Kanya ne ya sanar wa manema labarai a jiya ya ce hatsarin ya faru a daren ranar Litinin.

Kanya ya ce hatsarin ya faru ne ga motar kasuwa Avensis mai dauke mutane 11 ta kwacewa direba ta bugi icce.

Ya ce wadan da suka samu rauni suna kwance a babbar asibitin Gwadabawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *