Spread the love

Shugaban marasa rinjaye a majalisar dattijan Nijeriya Enyinnaya Abaribe ya yi kira shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi murabus saman kujerarsa ta shugaban kasa saboda matsalar tsaro da ta kara ta’azara a Nijeriya.

Ya yi wannan kiran ne a Laraba lokacin da majalisa ke tattauna kudiri kan tsaron kasa da kalubalensa da bukatar da ake da ita na sake fasalin tsaron Nijeriya.

Abaribe shi ne mutum na farko da ya fara Magana kan kudirin, ya ga laifin shugaba Buhari kan kasa magance matsalar tsaro da kasar ke fama da shi.

Haka ma dan majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Koko da Mayama da Shanga a majalisar tarayyar Nijeriya daga Kebbi ya bukaci Shugaba Buhari ya sauya manyan hafsoshin tsaron Nijeriya ganin sun kasa kuma har wa’adinsu yakare.

Ya bayyana yankinsa na fama da matsalar tsaron ‘yan bindiga sun je kasauwar Dadinkowa sun kori mutane. A kwanan nan an yi garkuwa da wani tsoho ana bukatar miliyan 90 akwai bukatar a tashi tsaye ga wannan matsalolin na tsaro.  

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *