Spread the love

Kisan Mutum (musulmi) na tattare da Hakkoki Wanda kusan Duk mai hankali idan ya zauna yayi nazari zai tabbatar ma da cewa, “koda an kashe Wanda ya kashe shi to babu shakka ya zalunchi Wanda ya kashe”

Dalili na farko Shi ne, duk mutum Dan Adam yana da burin da ya sanya a gabansa, da yake so ya cimma a duniya, Idan kazo ka kashe mutum hakika ka yanke masa cimma wannan buri da yake son ya cimma (Duk da cewa, Ko ka kyale shi lokacinsa zai yi), amma dai shi ne dalili na farko da malamai suke kallo a matsayin zaluncin da ka yi masa.

Abu na biyu, Idan magidanci ne kuma yana da ‘ya’ya to ka zalunce su, domin ka mayar da su marayu za su rasa tausayi da uba ko uwa ke yi wa ‘ya’yansu. Zasu rasa Add u’ar Alkheri da mahaifa ke yiwa ‘ya’yansu.

Ko ta wannan dalilin kawai za mu yi duba ga irin zalunchin da aka yiwa Wanda aka kashe.

Dalilin da zai sanya duk masoyin Maryam Sanda zai so a kashe ta shi ne, malamai Suna kyautata zaton muddin aka kashe Wanda ya kashe wani akwai yiyuwar Allah zai yafe masa.

Duk da wasu malamai suna ganin Allah ba zai yafe masa ba saboda fadan Allah (Swt) Inda yake cewa, “Kuma wanda ya kashe wani mumini da ganganci, to, sakamakonsa wutar Jahannama, yana madawwami a cikinta, kuma Allah Ya yi fushi a kansa, kuma Ya la’ane shi, kuma Ya yi masa tattalin azaba mai girma.” (qur’an:4:93).

Saboda a Kara nuna mana matsalar kisa Sai Manzon Allah (SAW) ya nuna mana ko kafirin Amana baza’a kashe dagangan ba.

Duk kuwa wanda ya kashe wani daga cikinsu da ganganci ba zai shiga Aljanna ba. Abdullah ibn Amru (RA) ya ruwaito cewa: “Manzon Allah (Saww) ya ce: “Duk wanda ya kashe wani mutum da yarjejeniyar zaman lafiya ta yi masa kariya, ba zai dandani kanshin Aljanna ba. Alhali hakika ana jin kanshin Aljanna a nisan tafiya shekarar arba’in.” (Buhari, Hadisi na 6516).

Babu shakka duk masoyin Maryam Sanda na gaskiya to kuwa zai so a wannan hukunci ya tabbata a kanta. Kusan ma tausaya Mata kan iya jefa mutum aikata lefi babba.

Dalili anan Sahabban Annabi (Saww) suna Bada labari cewa, basa ganin fushin Annabi (SAW) sai idan wani ya keta Haddin Allah.

Har An ruwaito cewa, Lokacin da wata mata mai daraja tayi sata aka zartar Mata da hukuncin kisa, sai Sahabbai suka tausaya Mata suka ga rashin dacewar hukuncin, Anan suka ga Fushin Annabi (SAW) Wanda basu taba ganin irinsa ba.

Saboda fushi Har Annabi (SAW) yace, Ya Rantse da Allah da ace fadima ‘yar Manzon Allah tayi sata wallahi da sai ya yanka hannunta.

Sannan ya zo a tarihi Cewa, Wani Yaro ya Kama karto a gidan wani mutume yana zina da matar mutane, Sai Kwarton da wannan Mata suka kamashi suka kashe shi.

Bayan asirinsu ya tonu aka kaiwa Sayyidina Umar (RTA) su nan take ya kashe su duka (matar da kwarton).

Anan wasu sahabbai Suka ce da sayyidina Umar (RTA) ya zaka yi haka bayan rai da rai aka ce (Ma’ana Annabsu bi Nabsu). Amma saboda sun kashe mutum rai guda sai ka kashe rai biyu.

Anan Sayyidina Umar (RTA) ya yi fushi yace dasu, “Wallahi da taron wayanda suka kashe yaronnan sun kai yawan mutanen San’a (Yemen), da duka sai na kashe su”

Wannan Zai tunana Mana ba’a tausayawa kowa akan hukuncin Allah tausayin da zakayi masa shi ne ka Bari a zartarda hukuncin Allah a Kansa.

A’uzubillahi Min zalik

Jamilu Sani Rarah Sokoto

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *