Spread the love

An kama likitan karya a Kano bayan ya shafe shekarru yana duba maras lafiya, likitan da aka bayyana na jabu ne yake cin karensa ba babbaka a Kano.

Hukumar kula da wuraren lafiya masu zaman kasnu(PHIMA) a karkashin ma’aikatar lafiya ta jiha a sintirin da suka gudanar da kungiyar likitoci(NMA) sun tona asirin mutumin mai suna Ibrahim Adamu.

Adamun ya ce shi kwararren likita ne wanda aka gano ba haka ba ne.

Sakataren hukumar Dakta Usman Tijjani Aliyu ya yi magana da manema labarai bayan an yi kamen ya ce sun sanyawa wanda ake zargin ido tsawon lokaci.

Ya ce an kama Adamu ne biyo bayan yawon asibiti da yake yi daga wannan zuwa wannan har makwabtan jihohi yake zuwa.

Dakta ya ce wanda ake zargin yana hannun ‘yan sanda domin gudanar da bincike.

Ya kara da cewar mai laifin ya aminta da laifinsa, ya ce takardun wani ne yake aiki da su da ya sace.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *