Spread the love

Tun Bayan da aka ZargI Maryam Sanda da Kashe Mijin ta Bilyaminu Bello Jama’a ke ta tofa Albarkacin Bakinsu na Ganin an Hukunta ta.

Shari’ar ta Ɗauki Lokaci Kafin Yankewa Maryam Hukumci a Yau Litinin, in da Mai Shari’a Justice Yusuf Haliru, ya yanke mata Hukunci a babbar kotu dake birnin Abuja.
Indai ba ku Mance ba shekara Baya ne Muka Kalato Maku Labarin Maryam Sanda Bisa Kashe Mijinta Bilyaminu Bello dan tsohon shugaban Jam’iyyar PDP, Alhaji Bello Haliru Muhammad.

Maryam na da damar daukaka Kara ga hukuncin da aka yanke mata ganin wannan kotu matakin farko ce ga Shari’a, wasu Shari’u masu Kama da wannan an yi ta gabatar da su a kotun koli abin da Managarciya ke kallon haka na iya faruwa kenana Shari’ar ta wuce wannan kotun kafin aminta da hukuncin.

In aka samu cikaken bayanin hukuncin da damar da Maryam ke da ita za mu kawo maku.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *