Spread the love

Tsohon Ciyaman a karamar hukumar Sokoto ta Arewa Alhaji Abdullahi Hassan ya yi hasashen kudi za su daina tasiri a zaben Nijeriya yau da gobe a ganinsa talaka zai waye ya daina karbar na goro a lokacin da ya zo rumfar zabe.

Ya fitar da bayaninsa ne a turakarsa ta facebook yau Lahadi bayan jam’iyarsa ta APC ta sha Kaye a zaben cike gurbi na ‘yan majalisar tarayya da jiha da aka gudanar a Sokoto ya ce da ya saye kuri’a ga hannun talaka don ya zabe shi gara a ce ba shi ya ci zabe ba.

“Da in saye kuri’a gara a ce bani na ci zabe ba. Yau da gobe kudi za su daina tasiri ga zabe har dai in talaka ya gano illar satar da ake yi masa.” Inji Abdullahi Mu’azu Hassan.

Wannan hasashe nasa yana da kamar wuya ganin yanda talakawa musamman mata suka mayar da ranar jefa kuri’a lokacin samo kudin kashi da yin an-ko. Matasan maza kuwa suna dauka ranar samu ce don canja riga ko sayen abinci mai dadi ko yi wa budurwa hidima.

Ranar jefa kuri’a duk Wanda ka ji kalamansa ina ne aka fi bayar da kudi ba ruwansu da sanin tsarin jam’iyyu na ciyar da jiha da kasa gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *