Spread the love

Hakika har yanzu jam’iyar APC rashen jihar Zamfara tana cigaba da jiran adalci akan kudurin sake duba hukuncin kotun koli kan shari’ar zaben na jihar zamfara wanda kotun koli ta gabatar a ranar 24 ga watan Maris na shekarar 2019 wanda ake ganin hukunci ya zo ne tare da mamaki, rashin adalci da kuma rashin bayyana gaskiya.

Tun lokacinda Kotun Koli ta Najeriya ta bayyana hukuncinta a kan zaben Jihar zamfara wanda ya kunshi hukuncin zaben Gwamnan zamfara, ‘yan majalisun tarayya na zamfara da kuma ‘yan majalisun dokokin jiha, ya zama abun cece-kuce a siyasar Najeriya wanda wasu al’umma da yawa suke ganin ba’a yi wa ‘yan takarar jam’iyar APC adalci ba, a wannan hukuncin duk da cewar su ne suka ci zaben su baki daya.

Hakan ya sa jam’iyar ta APC ta shigar da kuduri tare da neman kotun koli da ta yi duba akan kudirin jam’iyar don sake duba fasalin wannan hukunci nata, wanda yanzu haka miliyoyin al’ummar zamfara da sauran yan Najeriya suke jiran kotun koli don bayyana gaskiyar al’amari da sake tabbatarwa yan jam’iyar APC nasarar su wadda suka samu tun farko a zabe.

A irin wannan lokaci wanda al’ummar zamfara suka maida hankali sosai tare da rokon Allah akan samun nasarar APC da samun nasarar sanya Alkalai masu gaskiya da adalci a cikin wannan shari’a don jiran sauraren bayani na kudurin sake duba hukuncin kotun koli yana da kyau dukkan Alkalai da za su gabatar da wannan hukunci su yi shari’a akan gaskiya da Adalci domin ceto al’ummar zamfara daga hali na rashin tabbas wanda jihar ta fada wajen jiran hukuncin gaskiya a wannan shari’a.

Ra’ayi: Matasa Masu Kishin Jihar Zamfara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *